Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Batun kasar Sin ta nemi gafara game da COVID-19 ba shi da hujja
2020-03-05 21:18:13        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Zhao Lijian, ya karyata, ikirarin da wasu ke yi cewa, wai Sinawa su nemi gafara game da cutar numfashi ta COVID-19 da ta bulla a kasar. Ya jaddada cewa, annoba, abokiyar gabar daukacin bil-Adam ne, kuma kasar Sin kamar sauran kasashe da wannan cuta ta bulla, ita ma ta shafe ta, Don haka, batun wai kasar Sin ta nemi afuwa ma bai taso ba, kuma babu hujja a cikinsa.

Zhao wanda ya bayyana haka yayin taron manema labarai da ya gudana a yau Alhamis, ya ce, hukumar lafiya ta duniya ta sha bayyana cewa, nuna tsangwama ya fi illa a kan cutar kanta.

Ya ce, a wannan lokaci, mece ce manufar wasu mutane da kafofin watsa labarai na yada irin wadannan sanarwa na rashin kan gado? Yanzu haka, ba a gano asalin kwayar cutar ba. Ko ma daga ina wannan kwayar cuta ta samo asali, Kasar Sin, kamar sauran kasashe da wannan annoba ta bulla, ita ta shafe ta, tare da daukar matakan hana yaduwar ta. Hukumomin hana yaduwar cututtuka ta kasar Sin, suna kokarin sauke nauyin da ke bisa wuyanta. A kokarin da ake na kandagarki da hana yaduwar cutar, karfin kasar Sin, da managartan matakai a kan lokaci da kasar ta dauka, sun samu yabo daga kasashen duniya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China