![]() |
|
2020-03-05 20:10:20 cri |
A yayin da ake samun karuwar mutanen da suka kamu da cutar a wajen kasar Sin, abin damuwa game da cutar shi ne ba a san asalinta ba a wasu kasashe.
Wannan sabuwar cutar ta wuce saninmu a halin yanzu. Babban sakataren hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, "Ba mu san asalin annobar ba, ba mu san wane yanayin kwayoyin halittun cutar ba, kuma ba mu fahimci yadda take yaduwa na. Akwai bukatar sanin hanyar don warware wadannan matsaloli."
Abin bakin ciki shi ne, a yayin da ake nazarin cutar, saboda rukunin farko na wadanda suka kamu da cutar sun fito ne daga kasar Sin, sakamakon haka, wasu suka ce cutar ta samo asali ne daga kasar Sin, har ma wasu kasashe sun zargi kasar Sin ba tare da wata hujja ba, a cikin rahoton da wasu kafofin watsa labaru suka bayar ma sun kira cutar numfashin da suna "Cutar numfashin Wuhan" da "Cutar numfashi ta kasar Sin".
Irin wannan mataki na rashin hankali, ya gamu da adawa daga masana kimiyya. Jami'in hukumar WHO dake kula da ayyukan gaggawa Michael J Ryan ya ce, "Cuta na iya bulla a ko'ina". Cutar numfashi ta COVID-19 annoba ce ta duniya baki daya, kuma cutar kusan ta bulla a duniya baki daya."
Tun da har yanzu ba a iya tabbatar da asalin cutar ba. A hanlin yanzu ya kamata a yi kokarin hana yaduwar annobar, don kara ceton rayukan jama'a, abu mafi muhimmanci shi ne, a mai da hankali kan tinkarar wannan "Lamari na bakin ciki a tarihi". ( Mai fassara: Bilkisu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China