![]() |
|
2020-03-04 20:19:43 cri |
Rahotanni na cewa, yawan mutanen da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 yana ta karuwa, wasu kasashe ma na kara fuskantar matsin lamba wajen tinkarar annobar. Game da ayyukan da kasar Sin ta yi a kwanan nan na raba fasahohin da ta samu na kandagarki da shawo kan cutar, da kuma hanyar ba da jinya ga sauran kasashe, Zhao ya ce, a yammacin ranar 3 ga wata, ma'aikatar harkokin waje da hukumar lafiya ta kasar sun shirya taron musaya a tsakanin kwararru ta bidiyo tare da kasashen Azerbaijan, Belarus, Georgia, Moldova, Armenia, Turkmenistan da kuma kungiyar hadin kai ta Shanghai.
Baya ga haka, Zhao ya ce, kafin haka bangaren Sin da kungiyar EU sun shirya taro ta kafar bidiyo har sau biyu, don mu'amala sosai kan ayyukan kadangarki da shawo kan cutar.
Rahotannin sun ce, wasu kafofin watsa labaru sun ce, cutar ta samo asali ne daga kasar Sin, kuma an rubuta wasu kalmomi kamar "Kwayar cutar kasar Sin" da "Kwayar cutar Wuhan" a yanar gizo. Amma kuma akwai wasu rahotanni da ke cewa, akwai wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a cikin wadanda suka kamu da mura mai yaduwa a kasar Amurka. Game da haka, Zhao ya jaddada cewa, maganar da wasu kafofin watsa labaru ke cewa wai kwayar cutar numfashin "kwayar cutar kasar Sin" ce, wannan rashin mutunci ne, kasar Sin tana adawa da wannan. Yanzu haka ana kokarin binciken asalin kwayar cutar, kuma ba a samu sakamako ba. Hukumar WHO ta sha bayyana cewa, yaduwar cutar batu ne da ya shafi duniya baki daya, kuma har yanzu ba a tabbatar da asalinta ba, a wannan lokaci kamata ya yi a mai da hankali kan matakan hana yaduwarta, maimakon bata sunan wata kasa. (Bilkisu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China