2020-03-03 21:07:06 cri |
Jami'in wanda ya bayyana haka yayin taron manema labarai game da aikin kwamitin, ya ce, domin ganin bayan wannan cuta, an dauki managartan matakai masu karfi na hana yaduwa, kuma duniya ta kalli yadda gwamnati kasar Sin ta dauki matakan da suka dace, da karfin hadin kan al'ummar kasar da karfin tsarin kasar.
Da yake bayani game da nasarar da kasar ta ke fatan cimmawa a fannin raya kasa, biyo bayan bullar annobar COVID-19, Zhang, ya ce, a matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kasar Sin tana sane da nauyin dake bisa wuyanta, kuma tana daukar jerin managartan matakai, ciki har da manufofi na tallafi da ta dauka ta fannonin harkokin kudi, da haraji, da masana'antu, don ganin ma'aikata sun dawo bakin aiki da samar da yanayin da ya dace na ganin kamfanoni sun dawo aiki kamar yadda ya kamata, ta yadda za a bunkasa tattalin arzikin kasar.
Ya kara da cewa, kasar Sin za ta rage tasirin bullar cutar da yin aiki tukuru, don cimma nasarar manufar da ta sanya a gaba a fannin tattalin arziki da jin dadin jama'a.(Ibrahim)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China