Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An soma shirin daukar ma'aikata ta manhajar hoton bidiyo ta Yangshipin
2020-03-03 19:19:36        cri
Manhajar hoton bidiyo ta Yangshipin ta babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a takaice, ta hada kai da kamfanin raya kasa da zuba jari na kasar (SDIC), da hukumar sa ido da kula da kadarori ta kasa na majalisar gudanarwar kasar (SASAC), don soma shirin daukar ma'aikata ta kafar intanet a hukunce a yau Talata. Adadin ma'aikatan da ake son a dauka a karon farko ya kai kimanin 75,000.

Masu neman aikin dake zaune a gida suna iya shiga intanet don kallon bayanan fifikon kamfanoni da yadda matsayin aiki yake da takaitaccen bayani game da guraben aiki ta hanyar manhajar hoton bidiyon ta Yangshipin.

Wannan shiri ya mayar da hankali ne wajen warware matsalar rashin ma'aikata da rashin damar hayar ma'aikata da kamfanoni ke fuskanta a yanzu haka sakamakon cutar numfashi ta COVID-19 da ta bulla a kasar, inda aka yi amfani da fifikon kafar watsa labarai don inganta farfado da ayyuka da samar da kayayyaki. Ya zuwa yanzu, akwai sama da kamfanonin 1000 da suke son shiga wannan shiri, inda suke bukatar ma'aikata masu basira kimanin 75,000

A waje guda kuma, manhajar Yangshipin za ta kafa wani dandalin daukar ma'aikata na musamman ga daliban da za su kammala karatu a wannan shekara, ta yadda za a kawar da sabani dake akwai wajen samar da ma'aikata da hidimomi wato dalibai ba su da hanyar samun aiki, a nasu bangaren kamfanoni suna bukatar ma'aikata masu yawa. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China