Sabbin mutane 202 ne suka kamu da cutar COVID-19 a babban yankin kasar Sin
2020-03-02 10:15:43 cri
Hukumar lafiyar kasar Sin ta sanar a yau Litinin cewa ta samu rahoton sabbin mutane 202 ne suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 yayin da mutane 42 cutar ta hallaka a ranar Lahadin data gabata a babban yankin kasar Sin.
A cewar hukumar lafiyar kasar, dukkan mutanen da cutar ta kashe a ranar Lahadin daga lardin Hubei ne. (Ahmad Fagam)