![]() |
|
2020-03-01 20:18:43 cri |
Rahoton ya ce, kasar Sin ta dauki kwararan matakai daga fannoni daban daban, wadanda suka katse hanyoyin yaduwar cutar. Ban da haka, kasar Sin ta kuma yi amfani da fasahohin zamani da suka hada da kwaikwayon tunanin dan Adam da fasahar 5G da sauransu wajen warkar da mutanen da suka kamu da cutar. Baya ga haka, kasar Sin ta kuma samar da dimbin na'urorin kiwon lafiya tare da tura ma'aikatan lafiya sama da dubu 40 zuwa lardin Wuhan. Haka kuma al'ummar kasar Sin baki daya sun hada kansu wajen samar da gudunmawar kayayyaki ga lardin Wuhan. Duk wadannan sun burge masanan kwarai da gaske.
Kwalliya tana biyan kudin sabulu, kasar Sin ta fara samun saukin yanayin cutar. Duk da haka, cutar na yaduwa a sassa daban daban na duniya. Aikin da ya kamata kasa da kasa suka sanya a gaba shi ne su gaggauta daukar matakan dakile yaduwar cutar. Rahoton ya kuma jaddada cewa, matakan da kasar Sin ta dauka sun samar da darasi ga kasa da kasa wajen tinkarar cutar.(Lubabatu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China