2020-02-27 15:12:00 cri |
Kwanan nan, adadin kwantenonin cinikin wajen da aka yi dakonsu a lardin Hainan dake kudancin kasar Sin ya tasam ma na kwatankwacin lokacin bara. A nasa bangaren, mataimakin manajan sashin ayyuka na kamfanin kula da harkokion tashar jiragen ruwan dakon manyan kwantenoni dake Haikou, Lin Yi, ya bayyana cewa:
"Mun farfado da ayyukanmu tun satin da ya gabata, ya zuwa yanzu, muna iya kammala lodin kaya a cikin jiragen ruwa shida a kowace rana, kuma yawan kwantenonin da ake shige da ficensu a tashar ya kai dubu hudu a kowace rana."
Annobar cutar COVID-19 ta kuma kawo cikas ga ayyukan kamfanin Jialianheng, wani fitaccen kamfanin cinikin waje ne dake birnin Xiamen na lardin Fujian. A yayin da kamfanin ke matukar karancin kudaden shiga har yake dab da rushewa, hukumar harajin wurin ta fitar da wasu sabbin manufofi na dawowa gami da soke harajin da kamfanonin cinikin waje za su biya a lokacin yaki da annobar, al'amarin da ya taimaka sosai ga farfadowar kamfanin na Jialianheng. Mataimakin babban manajan kamfanin, Ye Siming ya ce:
"A da, sai mun shafe kusan rabin wata kafin mu samu kudin harajin da aka maido mana, amma yanzu, cikin kwana hudu kacal muka samu kudin har sau biyu, da yawansu ya zarce Yuan miliyan 20. Kudin da muka samu da wuri, ya sa mun kara rage hasarar da muka yi, kana za mu farfado da ayyukan kere-keren kamfaninmu ba tare da bata lokaci ba."
Har wa yau, a wasu lardunan kasar Sin wadanda harkokin cinikin waje suka yi fice, ciki har da Guangdong, da Jiangsu, da Zhejiang, da Shandong, an fitar da wasu manufofin musamman don tallafawa kamfanonin cinikin waje su warware matsalolin da suke fuskanta a fannonin hada-hadar kudi da jigilar kaya da kuma daukar ma'aikata. A nasa bangaren, mataimakin shugaban hukumar kasuwanci ta birnin Weifang na lardin Shandong, Wang Haotian ya nuna cewa:
"Mun yi bincike kan matsalolin da kamfanonin cinikin waje suke fuskanta, mun kuma warware su daya bayan daya, ta yadda hankalin kamfanonin zai kwanta su kuma ci gaba da gudanar da harkokinsu na kere-kere da kara samun kwastomomi."
Bugu da kari, ana farfado da kasuwancin kasa da kasa ta kafar intanet a sassa daban-daban na kasar Sin. Wani jami'in sashin hulda da jama'a na kamfanin Alibaba mai suna Cao Jie ya fayyace cewa:
"A lokacin bikin bazara, rassan rarraba kayan da aka shigo da su daga kasashen ketare dake biranen Tianjin da Ningbo da Hangzhou da Guangzhou sun yi aiki yadda ya kamata. Zuwa ranar 24 ga wata, dukkan rassan rarraba kayan da aka shigo da su daga ketare na Alibaba sun dawo bakin aiki. Kana, kamfanin Alibaba ya baiwa wasu kaya dubu 200 kudin rangwame wadanda aka shigo da su daga kasashen Koriya ta Kudu da Switzerland da Faransa da Spaniya da Jamus da Australiya da Japan, domin saukakawa masu sayayya."
A cewar ma'aikatar kasuwancin kasar Sin, za ta ci gaba da aiwatar da wasu muhimman dabaru a fannonin da suka shafi maido da kudin haraji a bangaren kayayyakin da aka fitar da su zuwa kasashen waje, da samun tallafin kudi a harkokin kasuwanci, da saukaka matakan cinikayya da sauransu, domin tallafawa kamfanonin cinikin waje, musamman wadanda ke gudanar da kasuwancin kasa da kasa ta kafar yanar gizo.
A nasa bangaren, mai taimakawa ministan kasuwancin kasar Sin, Ren Hongbin ya nuna cewa:
"Ga alama illar da cutar COVID-19 ta yi ga cinikin waje na wani dan lokaci ne, kuma harkokin cinikin waje na kasar Sin za su bunkasa cikin dogon lokaci, musamman akwai kamfanonin kirkire-kirkire da dama a kasar, don haka cutar ba za ta canza makoma mai haske ga harkokin cinikin waje na kasar Sin ba."(Murtala Zhang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China