Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na daukar matakan tallafawa masu sana'ar sayar da abinci da masaukai a gabar da ake yaki da cutar COVID-19
2020-02-26 19:08:28        cri

Ma'aikatar cinikayyar kasar Sin, ta ce mahukuntan kasar na ci gaba da daukar matakai daban daban, domin saukakawa masu sana'ar sayar da abinci da masaukai, a gabar da ake yaki da cutar COVID-19.

Da yake karin haske game da hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a yau Laraba, jami'i a ma'aikatar Xian Guoyi, ya ce an tanadi matakan samar da sauki, ta fuskar hada hadar kudi ga sassan biyu, duba da yadda bullar cutar ya haifar da matsin lamba gare su. Xian Guoyi ya ce za a dauke harajin VAT da sassan suke biya, domin ba su damar samun riba daga kasuwancin su. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China