2020-02-25 14:35:25 cri |
Bayan da tawagar kwararrun likitoci na Sin da WHO ta kammala rangadin aiki na tsawon kwanaki 9 a kasar Sin, tawagar ta kira taron manema labarai jiya Litinin a birnin Beijing, domin yin karin haske kan aikin da ta gudanar a kasar. Inda shugaban bangaren ketare na tawagar ya jinjina kokarin da Sin ke yi na yaki da cutar numfashi ta COVID-19, kuma ya nuna cewa, dabarun da Sin ke dauka a wannan fannin sun dace sosai, wadanda suka samu nasara.
A yayin taron manema labarai da aka shirya jiya, Liang Wannian, shugaban bangaren Sin na hadaddiyar tawagar kwararrun likitoci ta Sin da WHO, kuma shugaban kungiyar kwararru masu kula da aikin tinkarar cutar COVID-19 ta hukumar kiwon lafiyar Sin ya bayyana cewa, bayan da suka nazarci kwayoyin cutar COVID-19 guda 104 da aka samu daga wurare daban daban, ana iya tabbatar da cewa, ya zuwa yanzu kwayar cutar ba ta sauya ba. Ban da wannan kuma bayan da aka yi bincike kan kididdigar da abin ya shafa da ma rangadin da tawagar ta kai a birnin Beijing da lardunan Guangdong da Sichuan da ma Hubei, tawagar ta cimma daidaito kan cutar, cewar matsakaicin yawan shekarun masu kamuwa da cutar ya kai 51 da haihuwa, kaso 77.8 masu shekaru daga 30 zuwa 69 ne, kaso 77.5 kuma daga lardin Hubei. Game da batun cutar da ta samo asali daga jikin dabbobi, sakamakon nazarin ya shaida cewa, watakila cutar ta samo asali ne daga jemage, kuma dabbar pangolin ma na daya daga cikin dabbobin da ake iya samun cutar a jikinsu. Liang ya kuma furta cewa,
"Ruwa da miyau dake fitowa daga hanci da baki da kuma mu'amala, su ne manyan hanyoyin yada cutar COVID-19. Ana hasashen cewa, mai yiwuwa ne cutar tana yaduwa bayan da aka sha ruwa ko yin numfashin iskar da ta gurbata, sakamakon shigar najasar da ke dauke da kwayoyin cutar cikin iskar ko ruwan. Ban da wannan kuma akwai yiwuwar yada cutar ta hanyar iska wato yayin da aka yi tari ko atishawa da ke dauke da kwayoyin cuta."
A nasa bangaren kuma, Bruce Aylward, shugaban bangaren ketare na tawagar, kuma babban mashawarci na babban daraktan hukumar WHO ya bayyana cewa, a matakin farko, Sin ta dauki matakai kusan iri daya wajen yaki da cutar, daga baya kuma ta canja zuwa wasu dabarun kimiyya, bisa la'akari da hakikanin yanayin da ake ciki a wurare daban daban, da karfinsu na tinkarar cutar, har ma da wasu halayen musamman na yaduwar cutar. Babu shakka canja matakan sun yi babban tasiri. Yana mai cewa,
"Bayan da aka yi bincike daga fannoni daban daban a tsanake, tawagarmu tana ganin cewa, babu shakka kwararan matakan da kasar Sin ke dauka na dakile wannan sabuwar cutar sun hana tsanantar annobar cikin sauri. Yayin da na zo kasar Sin makwanni biyu da suka wuce, yawan masu kamuwa da cutar ya zarce dubu biyu a ko wace rana. Amma yayin da muka gama aikinmu, wannan adadin ya kai 416, wato adadin ya ragu da kashi 80 cikin dari, abin da nake so in jaddada shi ne, wannan adadi gaskiya ne, ganin yadda tawagarmu ta tabbatar da adadin raguwar bisa bayanan da muka samu daga hanyoyi daban daban. A waje daya kuma abubuwan da muka gane ma idanunmu su ma sun shaida gaskiyar raguwar adadin."
Haka zakila, Mr. Bruce ya yi tsokacin cewa, yayin bullar annobar, wasu na ganin cewa, tun da babu wani magani na hakika ko allurar rigakafin cutar, shi ya sa babu wata dabarar tinkarar cutar sai a zauna a jira abin da zai biyo baya. Amma abin da kasar Sin ke yi shi ne tun da babu magani, babu allurar rigakafi, muna iya yin duk abin da muka ga ya dace mu yi, muna iya ceton rayukan mutane bisa duk abin da muka ga ya dace. Hakikanin abun da ya shaida cewa, dabarar da Sin ke dauka tana da amfani, wadda ta samu nasara wajen dakile cutar. Bruce ya kara da cewa,
"Bisa nazarin da muka yi, muna ganin cewa, matakin da gwamnatin Sin ke dauka na tayar da duk al'ummar Sin tsaye na sassauta yanayin yaduwar cutar, wanda ya hana dubun-dubatar sabbin mutane daga kamuwa da cutar. Gaskiya, wannan wata babbar nasara ce mai matukar muhimmanci."(Kande Gao)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China