Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu sabbin wadanda suka kamu da cutar COVID-19, 397, yayin da 109 suka mutu
2020-02-22 16:36:08        cri

Hukumar lafiya ta kasar Sin, ta ce rahoton da ta samu a yau Asabar na nuna cewa, ya zuwa jiya Juma'a, an samu sabbin wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19, 397, yayin da 109 suka mutu, daga larduna 31 na kasar da jihar Xinjiang.

Rahoton ya tabbatar da cewa, ya zuwa jiyan, akwai sabbin wadanda suka kamu da cutar a lardin Hubei, inda cutar ta fara bulla, guda 366, yayin da 109 ya kasance adadin sabbin wadanda suka mutu.

Rahoton ya kawo adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a lardin Hubei da cutar ta fi kamari zuwa 63,454. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China