![]() |
|
2020-02-20 20:16:30 cri |
Michael Ryan, mai kula da aikin gaggawa a hukumar lafiya ta duniya ya yi nuni da cewa, yanzu haka adadin mutanen da suke kamuwa da cutar ya ragu, an samu nasarar haka, saboda gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan da suka dace.
Amma wasu kafofin watsa labaran kasashen yamma sun juya baya kan sakamakon da kasar Sin ta samu, inda suke zargin cewa, matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka a birnin Wuhan da sauran sassan kasar daya ne daga cikin ayyukan sarrafa al'ummun kasa mafiya tsanani a tarihi, zargin da ya kawo illa ga moriyar jama'a ta kasa da kasa.
Hakika ya zama wajibi a martaba kuma a kiyaye babbar moriyar jama'a, a don haka al'ummun kasar Sin suna kiyaye moriyar jama'a ta hanyar daukar matakan da suka shafi hakkinsu, duk wadannan sun nuna cewa, wayewar kan zamantakewar al'ummar kasar Sin ta samu babban ci gaba, annoba tana iya shafar daukacin bil Adama, a don haka, ya dace daukacin al'ummun kasashen duniya su hada kai domin ganin bayanta, kana ya dace a daina baza kwayar cutar siyasa ba tare da bata lokaci ba.(Jamila)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China