![]() |
| 2020-02-19 19:35:08 cri |
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a ba da muhimmanci wajen kare da ma kulawar da ta dace ga ma'aikatan lafiya, don tabbatar da cewa, suna cikin koshin lafiya, ta yadda za su mayar da hankali kan yakin da ake yi na ganin bayan cutar numfashi ta COVID-19 da ta bulla a kasar.
Xi, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban kwamitin koli na sojojin kasar, ya bayyana haka ne, cikin wani umarni na baya-bayan nan kan kare ma'aikatan lafiya dake aikin kandagarki da hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China