2020-02-19 14:17:29 cri |
Baya ga haka, jakadun kasashe da dama da ke kasar Sin sun bayyana goyon bayansu da ma fatan alheri ga kasar Sin, ciki har da jakadan kasar Rasha da na Jamus da Cuba da Iran da Brazil da Faransa da sauransu.
Akwai kuma shugabannin kasashen Afirka da suka aiko da sakwanninsu na nuna goyon baya ga kasar Sin.
Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari a sakon da ya aike ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, da daukacin al'ummar Sinawa, ya ce ko da yaushe Sin na goyon bayan Najeriya sosai, da ma nahiyar Afirka baki daya, inda a 'yan shekarun nan ma dangantakar ke kara fadada, don haka abu ne mai muhimmanci ga Sin ta san cewa, Najeriya da daukacin al'ummunta, na tare da ita a wannan lokaci na barkewar cutar covid 19. Shugaba Buhari ya ce yana da kwarin gwiwar cewa, Sin za ta shawo kan wannan annoba bisa ingantattun matakai da ake dauka.
Sai kuma shugaban jam'iyyar APC mai mulkin tarayyar Najeriya Adams Aliyu Oshiomhole, inda shi ma ya aikawa hukumar tuntubar kasashen waje ta kwamitin tsakiya ta JKS ta kasar Sin wani sako, yana mai bayyana goyon bayan kasarsa ga yaki da cutar numfashi da kasar ke yi. Adams Aliyu Oshiomhole ya nuna cewa, kamar yadda shugaban kasarsa Buhari ya bayyana cewa, matakan da Sin ta ke dauka na tinkarar cutar abin koyi ne ga sauran kasashen duniya. APC ta yi imanin cewa, gwamnatin Sin na da cikakken karfin shawo kai da kuma magance cutar. Yana kuma fatan gwamnatin kasar Sin da jama'arta za su cimma nasarar wannan yaki da ma hanzarta dawo da zaman rayuwar yau da kullum yadda ya kamata.
Baya ga haka, shugaban hukumar zartaswar kungiyar AU Moussa Faki,shi ma ya bayyana a cikin wasikar da ya aikewa shugaba Xi Jinping cewa, yayin da kasar Sin ta ke kokarin tinkarar cutar numfashi, kungiyar AU na tare da kasar Sin, tana kuma kiyaye hadin kan sassan biyu.
Duniya daya ce ga 'yan Adam baki daya. A cikin 'yan shekarun baya, manufar "gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkanin bil Adam"tana ta kara samun karbuwa tsakanin kasashen duniya,inda har aka sanya ta cikin kudurorin MDD. A yayin da al'ummar Sinawa ke iyakacin kokarin yaki da cutar numfashi ta Covid-19, tallafi da goyon bayan da gamayyar kasa da kasa suka ba kasar Sin, sun kuma bayyana abun da ake nufi da manufar.
A yayin da kasashen duniya ke kara dunkulewa da juna, matsalar wata kasa za ta iya shafar duniya baki daya cikin sauri.Duk da cewa cutar numfashi ta Covid-19 ta bulla ne a kasar Sin, ta shafi 'yan Adam baki daya. Tun bayan barkewar cutar, kasar Sin ta hada karfin sassanta daban daban,tare da daukar kwararan matakai masu inganci, sannan ta yi iyakacin kokarin dakile yaduwar cutar zuwa sauran sassan duniya, duk da cewa ta yi asara da dama, sabo da a ganinta, wannan nauyi ne da ya rataya a wuyanta.
Kamar yadda shugaban kasar Sin ya ce, bisa manufar gina al'umma mai kyakkyawar makomam ta bai daya, kasar Sin tana kokarin kare lafiyar al'ummarta da ma ta duniya baki daya. Ya ce an yi namijin kokari, kuma an dakile yaduwar cutar a fadin duniya. Ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da hada gwiwa da kasashen duniya, tare da bayyana halin da take ciki yadda ya kamata. Bisa tallafi da taimakon da kasa da kasa suka samar, tabbas kasar Sin za ta samu galaba a wannan yaki. (Lubabatu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China