2020-02-18 11:36:05 cri |
Mario Cavolo, dan italiya ne mazaunin Amurka, wanda yanzu yake zaune a birnin Shenyang na kasar Sin, ya rubuta wata mukala dangane da yadda kasar Sin ke fama da cutar numfashi ta COVID-19, da kuma yadda wasu kasashe ke kallonta.
A cikin mukalar tasa, ya tabo wasu muhimman batutuwa da ya kamata a yi la'akari da su idan ana batun barkewar cutar COVID 19 a kasar Sin.
Mario Cavolo, ya fara da cewa, a lokacin da aka samu barkewar murar Swine da ake kira H1N1 a Amurka a shekarar 2009, mutane miliyan 60 ne suka kamu da ita a kasar, inda kuma ta yi sanadin mutuwar a kalla mutane 18,449 a duniya a sannan. Kuma bisa kididdigar da cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Amurkar ta fitar daga bisani a shekarar 2012, kan a shawo kan cutar, adadin wadanda ta shafa ya zarce hakan, inda ta yi sanadin mutuwar mutane 300,000.
Ya ce wannan lamari ne ya sa shi yin tunanin dalilin da ya sa wasu 'yan adawa ke sukar kasar Sin da al'ummar Sinawa yayin da suka zage damtse wajen yaki da barkewar cutar COVID-19 da ta barke a birnin Wuhan na yankin tsakiyar kasar. Yana mai cewa, dole ne ya yi tambaya tare da amsa wasu tambayoyi.
Ya ce a lokacin barkewar murar H1N1, babu wani lamari na nuna kyamar Amurkawa da ya gani a fadin duniya da zai iya tuna. Hakika ma, sai da Amurka ta dauki watanni 6 kafin ta ayyana matakin tabaci kan cutar. Ya ce shin akwai wata gwamnati da tun daga lokacin da cutar ta barke a watan Afrilun 2009 har zuwa karshen Afrilun 2010, har zuwa watan Yuni, da kasar ta ayyana matakin tabaci kan cutar, da ta sanar da 'yan kasarta su bar Amurka? Shin kasar Sin ko Jamus ko Japan ko wata kasa ta daban, ta rufe iyakarsu ga matafiyan Amurka? Ya amsa da cewa, babu ko daya.
Mario Cavolo ya kara da cewa, ya lura bayan ma'aikatar kula da manufofin kasa ta Amurka ta ba Amurkawa shawarar ficewa daga kasar Sin, shi ma ofishin jakadancin Birtaniya, ya fitar da irin wannan sanarwa ga 'yan kasarsa.
Lamarin da ya sa shi tambayar, shi ko a shekarar 2009, 'yan asalin Birtaniya mazauna Amurka, sun samu irin wannan sanarwa daga kasarsu na su bar Amurka? Ya amsa da a'a.
Har ila yau, ya ce, shin kasashen duniya sun bada shawarar ware Amurka? Ko rufe iyakokin Amurka? Ya ce amsar ita ce 'a'a', babu wata kasa da ta bada wannan shawara.
Ya kuma tambayar ko Amurkawa sun fuskanci kyama ko wariya daga masu adawa da manufofin kasarsu kamar yadda Sinawa ke fuskanta a yanzu? Ya sake amsawa da a'a
A cewarsa, idan kai ma'aikaci ne dake zaune a kasar Sin yanzu haka, idan har ba a Wuhan kake ba, to gaskiyar magana ita ce, abu mafi aminci da kwanciyar hankali shi ne, zama a inda kake ba tare da tafiya ko ina ba. Ya ce babu inda za ka fi kasancewa cikin aminci da kwanciyar hankali fiye da wannan kasa, inda kusan kowa ke zaune a gida tare da kebe kansa bisa fahimta. Baya ga matakin da gwamnatin kasar Sin ta dauka na kare lafiyar al'umma da iyalai da daukacin jama'a, wanda abu ne da zai lakume daruruwan biliyoyi na tattalin arzikinta.
Daga karshe, ya ce bayani na hankali dangane da kwayar cutar COVID-19 da ta barke a Wuhan na kasar Sin shi ne, ba sunanta kwayar cutar Sin ba, kamar yadda ba a kira murar H1N1 kwayar cutar Amurka ba. Ya kara da cewa ko da za a dauki makonni 2 ko watanni 2 daga yanzu, wannan nau'in muran zai wuce, sannan a ci gaba da murnar shigowar lokacin bazara, kamar yadda ko wani yanayi na mura kan wuce. Sai dai, ya ce matakan da kasar Sin da Sinawa suka dauka tare, na dakile yaduwar cutar ya cancanta, domin da gaske ne cewa, wannan cutar numfashi ta COVID-19 ta fi murar da aka saba gani hadari, kamar dai yadda hadarin murar H1N1 yake a shekarar 2009. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China