Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shirin musamman da CMG ya gabatar ya karfafawa al'umma gwiwa
2020-02-09 20:00:33        cri

A jiya da dare, babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin(CMG) ya gabatar da shirin da aka hada musamman domin bikin Yuanxiao, bikin da ya alamanta kawo karshen bikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta Sinawa. Sai dai a wannan shekarar, a sakamakon cutar numfashi da kwayar cutar coronavirus ke haddasawa, an rage lokacin shirin zuwa awa daya da rabi, kuma an maida hankali a kan labaran da suke matukar sosa ran al'umma wadanda suka faru a yayin da al'ummar Sinawa suka himmantu wajen dakile yaduwar cutar, don nuna girmamawa ga masu aikin shawo kan cutar, tare da isar da sakon fatan alheri da kauna da kuma kwarin gwiwa ga al'ummar kasar.

Don kare yaduwar cutar, ba kamar yadda aka saba ba, a wannan karo, babu wani dan kallo ko daya a wurin daukar shirin, amma masu kallon shirin sun rubuta ra'ayoyinsu cewa, "Duk da cewa babu masu kallo a wurin daukar shirin, amma muna tare da ku, al'ummar Sinawa biliyan 1.4 na tare da ku." Shirin ya kuma samu yabo daga masu kallo, wadanda suka rubuta cewa, "Kwarin gwiwa ga dukkanin Sinawa! Kyakkyawar makoma za ta tabbata gare mu!" (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China