Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministocin harkokin wajen Sin da Masar sun tattauna kan hada hannu wajen yaki barkewar cutar Corona
2020-02-08 17:17:10        cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Masar, Sameh Shoukry a jiya, inda suka jadadda hadin gwiwar kasashensu wajen yaki da cutar numfashi ta Corona.

Sameh Shoukry, ya ce Masar na goyon bayan kokarin da kasar Sin take yi na yaki da annobar, kuma a shirye take ta taimaka iya karfinta, yana mai cewa, Masar ta yi ammana Sin za ta ci nasarar kawo karshen cutar.

Ya kara da cewa, har kullum, kasashen Afrika za su ci gaba da kasancewa tare da kasar Sin a lokacin da take cikin matsala.

A nasa bangaren, Wang Yi, a kokarinta na yaki da cutar, kasar Sin ba ta tsaya kan kare lafiya da tsaron Sinawa kadai ba, har ma da bada gudunmuwa wajen kula da lafiyar al'ummomin kasa da kasa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China