![]() |
|
2020-02-06 19:07:25 cri |
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta nuna godiya yau Alhamis ga abokan al'ummar kasar Sin daga kasar Indonesia, wadanda suke nuna kulawa da goyon bayan kasar Sin wajen yaki da annobar cutar numfashi. Madam Hua wadda ta bayyana haka ta kafar Intanet, ta kuma gayyaci manema labaru da su gaya wa wani dan sanda na Indonesia wanda ke karfafa gwiwa ga birnin Wuhan da annobar ta bulla cewa, kasar Sin, musamman ma Wuhan tana maraba da dukkan wadanda suke mara wa Wuhan baya da nuna sha'awa ga kasar Sin, na ganin bayan annobar. (Tasallah Yuan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China