Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
ECA ta bukaci kasashen Afirka da su rungumi manufofin raya tattalin arziki ta hanyoyin da ba sa gurbata muhalli
2020-02-04 09:33:32        cri
Hukumar MDD mai lura da tattalin arzikin Afirka ko ECA a taikaice, ta yi kira ga kasashen Afirka, da su zage damtse wajen tsara manufofin ci gaban su, tare da dora muhimmanci ga salon raya tattalin arziki mai kare muhalli daga gurbata, da samar da birane masu ingantaccen yanayi.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar a jiya Litinin, ta ce salon raya fasahohin zamani ta hanyar amfani da na'urori, ya ingiza ci gaban bil Adama zuwa matsayin ci gaban masana'antu kashi na 4.

Sanarwar ta ce nau'o'in iskar carbon mai gurbata iska na sauya yanayi matuka, tana kuma haifar da tasiri ga yanayin karuwar zafi ko raguwar sa a dukkanin sassan duniya, inda ake samun karuwar zafi, da annobar ambaliyar ruwa, da fari, da kalubale a fannin noma.

A don haka ya dace duniya ta sauya dabaru, muddin dai ana da burin samar da ingantaccen ci gaba. Daga nan sai sanarwar ta bayyana ci gaban masana'antu a matsayin abun dake zaburar da ci gaban tattalin arzikin manyan kasashen duniya. ECA ta jaddada cewa, dabarun ci gaban bil Adama na asali, na sauyawa sannu a hankali, sakamakon bunkasar fasahohin zamani da ake samu a daukkanin sassan duniya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China