![]() |
|
2020-02-03 12:59:58 cri |
Ma'aikatar kudi ta kasar Sin ta sanar a jiya Lahadi cewar, gwamnatin kasar Sin za ta samar da karin rancen kudi ga manyan kamfanoni domin ayyukan dakile cutar numfashi ta coronavirus da ta barke.
Ma'aikatar ta sanar cewa, za ta saukaka kudaden ruwa na basukan da za ta samar, wanda Bankin Jama'ar Sin zai bayar da rangwamen kashi 50 bisa 100 wanda bai zarce shekara guda ba domin taimakawa fadada ayyukan samar da kayayyakin kiwon lafiya a wannan lokacin da ake cikin matsanancin yanayi na yaki da annobar cutar numfashi.
Mataimakin ministan kudin kasar Sin Zou Jiayi ya nuna cewa, ma'aikatarsa za ta samar da rancen kudaden gami da rage kudin ruwa ga manyan kamfanonin a bangarorin samar da allurar rigakafi, da samar da magunguna, da kayayykin ayyukan kiwon lafiya.
Rancen kudaden da Bankin jama'ar Sin zai samar a matakin kasa da bankunan kananan yankuna a shiyyoyin da ake fuskantar tsanani zai bayar da sassauci ga kamfanonin dake samar da magunguna da sauran kayayyakin aikin lafiya na yau da kullum.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China