![]() |
|
2020-02-01 15:46:38 cri |
Li Keqiang, wanda kuma zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS ne, kuma shugaban tawagar kwamitin yakar cutar numfashin, ya kara da cewa, matakan da za a dauka sun hada da: da farko dai, a tsara shirin komawa aiki ba cikin sa'i daya ba, wato a yarda da tsawaita lokacin hutun a lardin Hubei. Sannan, a tsawaita lokacin hutun ga wadanda ke lardin Hubei yanzu haka, amma wajen aikinsu na wasu wurare daban daban, a wani bangare na kokarin maganin cutar. Na biyu kuma, a gudanar da aikin zirga-zirga yadda ya kamata, da ma mai da hankali kan aikin zirga-zirgar mutanen da batun ya shafa. Na uku kuwa shi ne bada muhimmnci kan rigakafin cutar a kan hanyoyin sufuri. Na hudu kuma, a mayar da hankali kan zirga-zirgar mazauna wuraren da cutar ta fi kamari. Na karshe kuwa shi ne, tabbatar da jigbe isassun ma'aikata wajen gudanar da wasu muhimman ayyuka, kamar wadanda suka shafi zirga-zirga da maganin cutar da dai sauransu. (Kande Gao)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China