2020-01-29 16:27:43 cri |
Daraktan cibiyar CDC na Afrika John Nkengasong, ya shaidawa manema labarai a hedkwatar AU cewa, Cibiyar na hada hannu da bangarori daban-daban, ciki har da cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta kasar Sin, game da barkewar kwayar cutar Coronavirus, da ta fara bulla a kasar.
Daraktan ya ce tuni aka fara amfani da tsarin tunkarar matsalar gaggawa ta AU da nufin dakile yaduwar cutar a nahiyar.
Da yake tsokaci kan Cote d'Ivoire da aka gano wani da ake zaton ya kamu da cutar, John Nkengasong, ya ce cibiyar CDC na tuntubar hukumomi a kasar.
Har ila yau, da yake jadadda yadda kwayar cutar Coronavirus ke saurin bazuwa, daraktan ya yabawa matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka wajen tunkarar yanayin. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China