Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bukaci a dauki matakan gaggawa don magance farin dango a Habasha da Kenya da Somalia
2020-01-27 17:27:02        cri
Ofishin gudanar da ayyukan jin kan al'umma na MDD (UNOCHA) ya bukaci a gaggauta daukar matakan magance matsalar farin dango dake bin hamada da suka mamaye gonakin kasashen Habasha, Kenya da Somalia, wanda ya kasance annobar kwari mafi muni a tarihi da ta afkawa kasashen uku na nahiyar Afrika.

Cikin sanarwar da ofishin na UNOCHA ya fitar yace, "Kasashen Habasha, Kenya da Somalia suna fuskantar matsananciyar annobar fari dake lalata amfanin gona wanda Kenya ba ta taba samun irinta ba cikin shekaru 70, yayin da Habasha da Somaliya basu fuskanci makamancin ibtila'in ba cikin shekaru 25."

Ofishin MDDr ya ce, annobar farin dango dake bin hamada "ta lalata daruruwan kilomita na amfanin gona a Habasha, da dubban hektocin yabanya a Somalia."?A ranar Juma'a, ma'aikatar aikin gona ta Habasha ta bayyana cewa farin dangon sun lalata gonaki sama da hekta 65,000 a fadin kasar ta Habasha cikin watannin da suka gabata.

Asusun samar da tallafin kudaden gaggawa na MDD (CERF), a makon jiya ya fitar da kudi kimanin dala miliyan 10 domin ayyukan yaki da annobar farin dango a gabashin Afrika.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China