Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Mozambique ya rantsar da sabbin gwamnonin larduna
2020-01-23 11:29:43        cri
Shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi, ya jagoranci rantsar da sabbin gwamnonin lardunan kasar 10, bayan babban zaben kasar na watan Oktobar shekarar bara.

Rahotanni sun nuna cewa, dukkanin gwamnonin 'yan jam'iyyar Frelimo mai mulkin kasar ne, wadanda a karon farko a tarihin kasar, suka lashe zaben larduna na kai tsaye.

An gudanar da wannan salon zaben ne dai, bayan yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, biyowa bayan yarjejeniyar da tsagin gwamnati ya cimma da babbar jam'iyyar adawa ta Renamo, game da rabon ikon sassan gwamnatin kasar.

Yayin bikin rantsuwar, shugaba Nyusi ya ce, sabuwar gwamnatin kasar za ta yi aiki bisa tsarin rarraba iko tsakanin gwamnatin tsakiya da sauran larduna, kuma sauye sauye da gwamnatin za ta aiwatar, na da nufin shigar da dukkanin sassan kasar cikin sha'anin mulki, da kuma ingnata samar da hidima ga daukacin al'ummar kasar.

Daga nan sai ya yi kira ga sabbin gwamnonin, da a ko da yaushe, su yi aiki kafada da kafada da gwamnatin tarayyar kasar, su kuma kasance masu tsumin lalitar hukuma, tare da yakar cin hanci da rashawa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China