Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO za ta ci gaba da tattaunawa game da cutar numfashi da ta bulla a Sin
2020-01-23 10:17:05        cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce za ta ci gaba da gudanar da taron ta na gaggawa a yau Alhamis, bayan da masu ruwa da tsaki suka shafe yammacin Laraba suna tattaunawa, game da cutar numfashin nan da ta bulla a kasar Sin. WHO na duba yiwuwar ayyana cutar a matsayin barazana ga harkar kiwon lafiyar kasa da kasa ko akasin hakan.

Yayin wani taron manema labarai bayan kammalar tattaunawar sirri da sassan masu ruwa da tsaki, babban daraktan hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce an gudanar da tattaunawa mai armashi, to sai dai kuma akwai bukatar samun karin bayanai, muddin ana fatan cimma matsaya.

Tedros ya ce ya gamsu matuka, da cikakkun bayanai da bangaren Sin ya samar game da wannan cuta, da ma yanayin yaduwar ta. Ya ce hukumomin Sin sun yi namijin kokari wajen daukar matakan dakile yaduwar wannan cuta mai hadari.

Babban daraktan na WHO ya ce, Sin ta gayyaci kwararru daga hukumar zuwa birnin Wuhan inda cutar ta fara bulla, don haka WHO na da karin bayanai da za a baje kolin su a Alhamis din nan. Ya kuma yi fatan Sin za ta ci gaba da raba bayanan da ta tattara da sauran sassa, duba da cewa baya ga taimakawa ita kan ta Sin din, hakan zai kuma tallafa wajen dakile yaduwar cutar a matakin kasa da kasa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China