Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Sin da Myanmar sun kaddamar da bukukuwan cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin su
2020-01-17 22:00:20        cri

Da yammacin yau Juma'a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Myanmar Wen Myint, da shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi, suka jagoranci kaddamar da jerin bukukuwan murnar cika shekaru 70, da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, da kuma bikin shekarar yawon shakatawa ta kasashen biyu a birnin Naypyidaw fadar mulkin Myanmar.

Bayan kafuwar jamhuriyar al'ummar kasar Sin, Myanmar ce kasar ta farko dake da tsarin mulki na daban da ta amince da sabuwar kasar Sin. A shekarar nan kuma ta 2020, ake bikin cikar kasashen shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyya. Sassan biyu za su gudanar da jerin bukukuwan murnar cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin su, domin fadada musaya, da inganta hadin gwiwa a fannonin raya ilimi, da addini, da fannin watsa labarai, da samar da fina-finai da shirye-shiryen talabijin da ma sauran fannoni.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China