Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya gana da shugabar gwamnatin Myanmar
2020-01-17 19:53:37        cri

Da yammcin yau Juma'a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi, bayan bikin tarba ta musamman da shugaban Myanmar Win Myint ya yi masa.

Aung San Suu Kyi ta isa fadar gwamnatin Myanmar, inda ta yi wa shugaba Xi Jinping maraba da zuwa. Daga bisani kuma suka yanke shawarar gudanar da shawarwari a tsakaninsu a gobe Asabar. Ana kuma fatan za su sake ganawa da juna a gobe Asabar, inda za su zurfafa shawarwari, game da muhimman batutuwan da suka shafi Sin da Myanmar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China