Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Djibouti ya jaddada fatan kara bunkasa hadin gwiwar kasarsa da Sin
2020-01-10 09:46:07        cri
Shugaban kasar Djibouti Ismail Omar Guelleh, ya jaddada fatan kara bunkasa hadin gwiwar kasarsa da Sin, a fannonin raya tattalin arzikin teku, da dabarun amfani da na'urori masu kwakwalwa wajen samar da ci gaba.

Ismail Omar Guelleh, ya bayyana wannan fata ne a jiya Alhamis, yayin ganawarsa da dan majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi. Ya ce muhimmiyar alakar dake tsakanin kasarsa da Sin ta cancanci yabo, kuma gwamnati da jama'ar Djibouti, na godiya bisa tallafin da Sin ke samarwa kasar a fannonin raya tattalin arziki, da ci gaban zamantakewar al'umma.

Shugaba Guelleh ya kara da cewa, kasarsa dake kahon Afirka, na fatan kara shiga a dama da ita cikin shawarar ziri daya da hanya daya, da wanzar da ayyuka masu nasaba da kudurorin nan guda 8, wadanda aka amince da su, yayin taron dandalin FOCAC na shekarar 2018 da ya gudana a birnin Beijing.

A nasa bangare, Wang Yi ya ce, muhimmin hadin kai dake wakana a tsakanin Sin da Djibouti ya haifar da babban ci gaba, kuma Sin har kullum a shirye take, ta yi aiki da Djibouti, wajen tabbatar da nasarar ayyuka, kamar layin dogo tsakanin Djibouti zuwa Habasha, da tashar jiragen ruwa ta Doraleh, ta yadda Djibouti za ta ci gajiya daga fannonin tattalin arziki, da na kyautata rayuwar al'umma.

Ya ce Sin na fatan irin wadannan ayyuka na raya layukan dogo, da gina tashar jiragen ruwa, da kafa yankin cinikayya maras shinge, za su mayar da Djibouti cibiyar cinikayya da samar da hidimomi, wanda hakan zai ba kasar damar samun ci gaba mai tsari.

A wani ci gaban kuma, a dai ranar ta Alhamis, Wang Yi ya zanta da takwaransa na Djibouti Ali Youssouf, kafin daga bisani su gudanar da taron 'yan jarida na hadin gwiwa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China