![]() |
|
2020-01-09 09:53:44 cri |
An tabbatar da mutuwar mutane 4, sanadiyyar wata gobara da ta tashi a cikin wani gida a garin Damaturun jihar Yobe, dake arewa maso gabashin Nijeriya.
Yaro 1, mai shekaru 5 ya tsira da munanan raunika a gobarar da ta auku da daren ranar Talata, inda tuni aka garzaya da shi wani asibiti dake birnin.
Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar, Usman Habu, ya shaidawa Xinhua cewa, ana gudanar da bincike domin gano musabbabin gobarar.
Wani jami'in ba da agajin gaggawa ya ce, akwai yiwuwar lamarin ya auku ne saboda rashin wata kofa ta baya, da za ta kasance hanyar fita idan bukatar gaggawa ta taso. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China