Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattalin arzikin kasar Sin yana bunkasa yadda ya kamata
2019-12-25 20:59:51        cri
A yau Laraba, babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya gabatar da sharhi mai taken "Tattalin arzikin kasar Sin dake da makoma mai kyau, kuma cike da karfi yana bunkasa yadda ya kamata".

Sharhin ya nuna cewa, a shekarar 2019, ko da yake tattalin arzikin kasar Sin ya fuskanci wasu 'yan sauye-sauye a cikin gida da waje, amma ya jure duk wani matsin lamba, kuma ya gudana yadda ya kamata, kana an samu kyautatuwar tsarin da ingantuwar tattalin arzikin kasar cikin sauri, zaman rayuwar jama'ar kasar ma ya kyautatu, ana iya cewa, tattalin arzikin kasar na da makoma mai kyau, kuma yana cike da karfi.

Sharhin ya kuma ce, karfin tattalin arzikin kasar Sin ya dogaro ne kan babbar kasuwar kasar da bukatun cikin gida, da nasarorin da kasar ta samu a cikin shekaru 40 da aiwatar da manufar yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, da kuma manufar gwamnatin kasar ta neman bunkasuwa ba tare da tangarda ba.

Baya ga haka, sharhin ya nuna cewa, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin yadda ya kamata a cikin shekarar 2019, ba kawai ta karfafa imanin jama'ar kasar kan makomarsu ba, har ma ta ba da tabbaci ga tattalin arzikin duniya da ke fuskantar rashin tabbas. Idan aka yi hasashen shekarar 2020, za a ci gaba da fuskantar kalubale a cikin gida da ketare, amma duk da haka yanayin ci gaban tattalin arzikin kasar yadda ya kamata cikin dogon lokaci ba zai canja ba. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China