Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rasha: Wakilan NATO suna nuna karfin iko kan shawarar da aka yanke a WADA
2019-12-24 13:25:03        cri

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya bayyana aikinsa a jiya Litinin a gun taron majalisar dattawa, inda ya ce hukumar yaki da shan magunguna masu kara kuzari ta kasa da kasa WADA, na yanke shawara bisa wani dalili na siyasa don illata ikon Rasha, kasancewar kasashen NATO ne ke jagorancin ayyukan hukumar.

Sergei Lavrov ya kara da cewa, mutane 15 ne ke da ikon ba da shawara a hukumar, 11 daga cikinsu na daga NATO, 2 kuma daga Austriliya da Japan, sai kuma sauran 2 daga Afrika da Latin Amurka. Ya ce yayin da wasu mutane masu yunkurin hana bunkasuwar Rasha ke yin hadin kai don kada kuri'u kan batun magungunan kara kuzari, Rasha na ganin cewa, suna yanke shawara ne bisa wani dalili na siyasa.

A baya dai WADA ta zargi Rasha bisa bita kan sakamakon da aka samu na gwaji kan magungunan kara kuzari da 'yan wasanta suka yi amfani da su, kuma ta yanke shawarar hana Rasha shiga wasanni har tsawon shekaru 4.

A kuma ranar 19 ga wannan wata, hukumar yaki shan magungunan kara kuzari ta Rasha, ta yi shirin kai kara a gaban kotu mai bincike harkokin wasannin motsa jiki na kasa da kasa kan wannan lamari. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China