Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na da karfin cimma karin nasarori bisa tsarin "kasa daya, tsarin mulki biyu"
2019-12-20 20:48:08        cri

 

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da jawabi a yau Juma'a, a yayin bikin murnar cika shekaru 20 da dawowar yankin Macao a hannun babban yankin, da bikin rantsuwar da jami'an gwamnatin yankin karo na 5 suka yi.

A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya waiwaye game da ci gaban da yankin ya samu, wajen gudanar da tsarin "kasa daya, tsarin mulki biyu". Abubuwan da suka shaida cewa, wannan tsari ba ma kawai ya daidaita matsalolin yankin Hong Kong da Macao da suka rage ba, har ma ya tabbatar da bunkasuwar yankuna cikin wadata a dogon lokaci, bayan dawowarsa hannun babban yankin.

A matsayin yanki na musamman dake da fili karami, amma da mutane da yawa, har ma da karancin sana'o'i, Macao ya kai ga samun bunkasuwa cikin sauri a cikin wadannan shekaru 20 da suka gabata, ta dogaro da wannan tsari. A cikin jawabin nasa, Xi ya takaita fasahohi 4 a fannin aiwatar da tsarin a yankin Macao, wato na farko, nacewa da kuma amincewa da wannan tsari. Na biyu kuwa, bin hanyar da ta dace wajen gudanar da wannan tsari. Sai na uku, wato tsayawa tsayin daka kan cika alkawarin dake cikin wannan tsari, sai kuma na karshe, wanda shi ne tsayawa kan tabbatar da tushe mai inganci a bangaren al'umma, da siyasa dangane da tsarin.

Abun lura dai shi ne, wannan tsari ya samu ci gaba mai kyau a Hong Kong da Macao, amma wasu sassan ketare ba sa son ganin ci gaban kasar Sin. Don haka sun hada baki da masu bore a Hong Kong, don tayar da zaune tsaye a yankin, don karyata wannan tsari, da illata bunkasuwar kasar Sin.

Game da hakan, Xi Jinping ya yi kira cewa: gwamnati, da kuma jama'ar kasar Sin, na da niyyar kiyaye tsarin mulki da tsaro da muradun kasar, kuma ko kadan, ba wanda zai iya tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar ta Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China