Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Aminu Bashir Wali: Bai kamata sauran kasashe su tsoma baki cikin harkokin Hong Kong ba
2019-12-09 14:03:38        cri


Aminu Bashir Wali, tsohon ministan harkokin wajen tarayyar Najeriya ne, wanda ya taba zama jakadan Najeriya dake kasar Sin. A lokacin da yake aiki a Sin, ya taba ziyartar yankin Hong Kong na kasar, inda ya ganema idanunsa yadda ake aiwatar da manufar "kasancewar kasa daya amma tsarin mulki biyu" a yankin. Malam Aminu Wali ya ce, tashe-tashen hankalin da suka barke a Hong Kong sun bakanta masa rai sosai, inda kuma ya jaddada cewa, harkokin yankin harkokin cikin gida ne na kasar Sin, wadanda bai kamata sauran kasashe su yi shisshigi a cikin su ba.

Aminu Bashir Wali ya taba aiki a matsayin wakilin tarayyar Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya. Tun daga shekara ta 2009, ya zama jakadan kasar dake Sin, sa'an nan kuma daga shekara ta 2014 zuwa 2015, ya zama ministan harkokin wajen Tarayyar Najeriya. A kwanakin baya ne, Wali ya zanta da kafofin watsa labarai a Abuja, inda ya bayyana ra'ayinsa game da hargitsin da ya wakana a Hong Kong, yana mai cewa:

"Ina matukar rashin jin dadi game da abun da suka wakana kwanakin baya a Hong Kong. Hong Kong cibiyar kasuwanci ce ta kasa da kasa, kana cibiyar tattalin arziki ce mai matukar muhimmanci a duk duniya, wadda ba kawai tana yiwa kasar Sin aiki ba ne, har ma tana aiki ga duk duniya. Rikicin da ya barke a Hong Kong abu ne maras kyau, amma ina da yakinin cewa gwamnatin yankin Hong Kong, za ta iya maido da yanayin doka da oda duk da cewa ana bukatar lokaci."

Yayin da yake zantawa kan mutane ko kuma kasashen dake goyon bayan masu ta da rigima a Hong Kong, Aminu Wali ya bayyana cewa:

"Ni na amince da wannan abu, wato akwai wasu kasashen ketare wadanda ke yunkurin yin shiga sharo ba shanu cikin harkokin yankin Hong Kong. Akwai wasu mutane ko kasashe wadanda suka kulla makarkashiya don rura wutar rikici a Hong Kong. A hakikanin gaskiya wannan abu a bayyane yake, kowa na iya fahimtar mene ne ainihin matsalar, wato idan ka san majalisar dokokin Amurka ta zartas da doka kan hakkin dan Adam da demokuradiyya na Hong Kong na shekara ta 2019, za ka iya gano dalilin da ya sa rikici ya barke a Hong Kong."

Malam Wali ya ci gaba da cewa, bai kamata sauran kasashe su yi katsalandan cikin harkokin cikin gidan kasar Sin ba, inda ya ce:

"Kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan manufarta ta rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe. A ra'ayina batun Hong Kong harkar kasar Sin ne zalla, ya kamata kasa da kasa su karfafa gwiwar babban yankin kasar Sin da Hong Kong, don su warware matsala da kansu, a maimakon hura wutar rikici."

A matsayinsa na tsohon gogaggen jami'in diflomasiyya, kuma masanin dangantakar kasa da kasa, Aminu Wali ya ce, ba zai yiwu ba kasashen yammacin duniya su rika zama ginshikan harkokin siyasar duniya a nan gaba, wato kamata ya yi su koyi yadda za su fadada hadin-gwiwa tare da wasu sabbin kasashe masu tasowa ciki hadda kasar Sin, domin shimfida zaman lafiya da tsaro a fadin duniya. Wali ya ce:

"Amurka babbar kasa ce da ta fi kowace karfi a duniya a halin yanzu, amma al'amuran na canjawa ko da yaushe. Birtaniya ma ta taba zama wata babbar daula mai tasiri, sabanin yadda al'amarin yake a halin yanzu. Saboda haka, ya kamata mu yi nazari sosai kan tarihin ci gaban duniya. Ina ganin cewa, kasashen da suke tsoma baki cikin harkokin yankin Hong Kong, sun aikata wani babban kuskure, saboda abubuwan da suka faru a Hong Kong, kila su iya faruwa wata rana a wadannan kasashe."(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China