Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin ruwan Libya sun ceto bakin haure 107 daga gabar tekun yammmacin kasar
2019-11-25 09:35:24        cri

Dakarun sojojin ruwan kasar Libya sun ce sun yi nasarar ceto bakin haure 107, yayin wani sintiri da suka gudanar a ranar Lahadi. Sojojin ruwan sun ce da fari sun ceto mutane 57 dake kokarin ketara gabar tekun kasar, daga bisani kuma suka ceto karin wasu 'yan ci ranin su 50 dake kunshe da al'ummu daga kasashen Afirka daban daban.

Da yake shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua hakan, kakakin rundunar sojin ya ce, an garzaya da wadanda aka ceto din zuwa cibiyar tattara bakin haure dake birnin Tripoli, fadar mulkin kasar.

Gabanin hakan, a ranar Asabar ma sojojin ruwan sun gudanar da sintiri a yankunan tekun kasar, inda a karo biyar, suka ceto 'yan ci rani dake yunkurin tsallaka gabar tekun kasar ta yammaci, wadanda yawan su ya kai mutane 383.

A ranar 22 ga watan Nuwambar nan, hukumar MDD mai lura da 'yan ci rani ko IOM a takaice, ta yi kira ga tarayyar Turai, da tarayyar Afirka ta AU, da su sauya salon da suke bi na magance kalubalen 'yan ci rani dake yada zango a Libya. IOM ta kiyasta cewa, sama da 'yan ci rani ta barauniyar hanya 8,600 ne aka mayar cibiyoyin tsugunar da su dake makare da jama'a a Libya, yayin da kuma MDD ke cewa, irin wadannan 'yan ci rani na rayuwa cikin wani yanayi da ya keta hurumi da hakkokin bil Adama. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China