Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasar Algeria
2019-11-18 09:42:22        cri
Jiya Lahadi aka kaddamar da gangamin yakin neman zaben shugaban kasar Algeria inda 'yan takara biyar za su fafata a zaben da za'a gudanar a ranar 12 ga watan Disamba

A wannan rana, 'yan takarar 5 sun rattaba hannu kan dokokin zabe wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ta tsara, dokokin sun shafi ka'idoji da nuna halayya ta gari wadanda suka shafi yadda za'a gudanar da zaben lami lafiya.

Duk 'yan takarar sun yi alkawarin za su tabbatar da mutunta fanni doka da oda a kasar, da bunkasuwar tattalin arzikin kasar ta hanyar fadada hanyoyin tattalin arziki wanda bai shafi man fetur ba, kuma za su kyautata yanayin zaman rayuwar al'ummar kasar Algerian ta hanyar warware muhimman batutuwan dake shafar kasar, da suka hada da matsalar rashin ayyukan yi da samar da gidaje, da samar da wani shirin musamman don tallafawa rayuwar masu karamin karfi, da mutane masu bukatar musamman, da wadanda suka yi ritaya daga aiki.

Za a shafe makonni biyu ana gangamin yakin neman zaben.

Domin tabbatar da samun ingantaccen zabe mai tsabta, an amince da kafa hukumomin sanya ido da tabbatar da dokokin zaben kasar, kamar yadda shugaban kasar na rikon kwarya Abdelkader Bensalah ya bayyana. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China