![]() |
|
2019-11-16 16:42:22 cri |
Jack Ma, mai rukunin kamfanin Alibaba, daya daga cikin manyan kantunan sayayya ta intanet na kasar Sin, ya yabawa dukkan masu lura da gandun dajin Afrika sabo da kokarin da suke wajen kula da dabbobin daji.
Yace yayi imanin cewa masu kula da gandun daji su ne ainihin jarumai na hakika a duniya. Banbancin dake tsakanin su da sauran mutane shine yayin da mutane ke baiwa kansu kariya, su kuma sun dukufa ne wajen bada kariya ga dabbobin daji. Suna da matukar bambanci da sauran jama'a, inji shi.
An gudanar da bikin karrama masu kula da gandun dajin ne a Accra, babban birnin kasar Ghana, a matsayin wani bangare na shirye shiryen da gidauniyar Jack Ma ta bullo da su don wayar da kan al'umma game da alakar dake tsakanin cigaban bil adama da kula da muhalli.
Ya bayyana kyakkyawar fata game da makomar Afrika sakamakon yadda matasan nahiyar ke mayar da hankali wajen kokarin kafa sana'o'in dogaro da kansu, sannan ya bukaci a gudanar da tsare tsaren cigaban dan Adam tare da cigaban muhallin halittu tare da juna.
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China