Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Labaran mata da yara daga yankuna daban daban na duniya, musamman ma a nahiyar Afirka
2019-11-19 15:17:48        cri

Yara sama da 85500 ne ba su zuwa makaranta a yankunan da ake rikici na Kamaru

Asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF) ya bayyana cewa, kimanin yara 855,000 ne ba su zuwa makaranta a yankin arewa maso yammaci da yankin kudu maso yammacin kasar Kamaru, sakamakon tashin hankalin da aka shafe shekaru uku ana yi a wadannan yankuna.

Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric, ya ruwaito wasu alkaluma na asusun na UNICEF na cewa, a cikin watanni biyu na sabuwar shekarar karatu, kimanin kaso 90 cikin 100 na makarantun firamaren gwamnati a wadannan shiyyoyi biyu, gami da kaso 77 cikin 100 na sakandaren gwamnati ne aka rufe ko ba a koyarwa.

Ya ce, muddin bangarorin da rikicin ya shafa ba su dauki matakan da suka wajaba na kare harkar ilimi ba, hakika makomar wadannan yara na cikin hadari.

A halin da ake ciki, asusun na UNICEF, ya bullo da wani shiri na koyarwa na al'umma, inda ake samarwa yaran kayayyakin koyo da amfani da gidajen rediyo don yakar jahilci da ba da darussa don taimakawa yaran, yayin da ba su zuwa makaranta.

Sudan ta Kudu ta rasa yara 7,640 sanadiyyar cutar limonia a 2018

Cutar limonia na sanadin mutuwar yaro guda cikin kowacce sa'a 1 a Sudan ta Kudu, lamarin da ya haifar da mutuwar yara 7,640 'yan kasa da shekaru 5 a bara.

A cewar wani rahoto kan nazarin mace-macen yara da asusun kula da kananan yara na MDD da kungiyoyin Save the Children da Every Breath Counts Coalition suka hada, cutar limonia na daya daga cikin abubuwan da suka fi kashe yara a Sudan ta Kudu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar kaso 20 bisa dari na yara 'yan kasa da shekaru 5 a shekarar 2018, saboda rashin daidaito da fatara da rashin samun kiwon lafiya.

Rahoton da hukumomin suka fitar, ya ce yaran da garkuwar jikinsu ba ta da karfi saboda wasu cututtuka ko kuma tamowa da wadanda suke yankunan dake da matsanancin gurbatar iska da rashin tsabtattacen ruwa, su ne suka fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar.

A cewar daraktar kungiyar Save the Children a Sudan ta Kudu, Rama Hansraj, asibitoci a Sudan ta Kudu na fama da yawan masu cutar limonia, wadda ta yi sanadin mutuwar yara 7,000 a bara.

Kwayoyin cuta na bacteria ko virus ne ke haifar da Limonia, inda suke wahalar da yara wajen yin numfashi saboda huhunsu ya cika da kwayoyin cuta da kuma ruwa.

MDD da Tanzania sun hada gwiwa don yaki da cin zarafin mata

Hukumar kula da al'amurran mata ta MDD mai fafutukar samar da daidaito a tsakanin jinsi da bunkasa sana'o'in dogaro da kai ga mata, ta yi hadin gwiwa da gwamnatin kasar Tanzania domin yaki da cin zarafin mata, wani babban jami'in hukumar ya tabbatar da hakan.

Faustine Ndugulile, mataimakin ministan lafiya da ci gaban al'umma, da kula da batun jinsi, da tsofaffi da kananan yara na kasar Tanzaniya ya ce, tun bayan da aka kaddamar da hadin gwiwar, adadin laifukan cin zarafin da ake yiwa mata ya yi matukar raguwa a kasar.

Jami'in ya ce, kimanin laifukan da suka shafi nuna wariya da cin zarafin mata 41,000 aka samu a fadin kasar cikin shekarar 2017, amma bayan yunkurin da aka yi karkashin hadin gwiwa tsakanin hukumar kula da al'amurran mata ta MDD da gwamnatin Tanzaniyan, matsalolin sun ragu matuka.

Hukumar kula da al'amurran mata ta MDD dake Tanzania ta shirya wani taron karawa juna sani a Dodoma, babban birnin kasar, domin zaburar da 'yan majalisu game da yadda za su ba da gudunmowarsu a yakin da ake da take hakkokin mata.

Ndugulile ya ce, a halin yanzu gwamnatin kasar tana shirin aiwatar da wani muhimmin shiri na shekaru biyar wato 2017/2018-2021/2022 da nufin lalibobi muhimman hanyoyin dakile laifukan cin zarafin mata.

Ndugulile ya bukaci 'yan majalisun dokokin kasar da su taimaka wajen kawo karshen munanan al'adu da suka shafi tsarin gargajiya a tsakanin al'umma wadanda ke kara rura wutar laifukan take hakkokin mata da nuna wariyar jinsi.

WHO ta yi kira da a samar da wani dandali na gama gari da zai inganta kiwon lafiya

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yi kira da a samar da dandalin da dukkan al'umma za su iya shiga a dama da su, domin gaggauta samun nasarar muradun ci gaba masu dorewa da ake son cimmawa a bangaren lafiya.

Tedros Adhanom Ghebreyesus, Darakta Janar na WHO, ya shaidawa wani taron kiwon lafiya a Nairobi cewa, idan kasashen duniya na son hidimomin kiwon lafiya su isa ko ina, to dole ne a ba bukatun wadanda da aka bari a baya muhimmanci, ciki har da mata da yara da matasa.

Ya ce WHO na kira ga kowacce kasa, ta kafa wani dandali da zai kunshi kowa da kowa, wanda zai hada mutane daga dukkan fannonin kungiyoyin al'umma da bangarori masu zaman kansu da malamai da iyayae da mutane masu rauni kamar mata matalauta da yara, don su tattauna da mambobin majalisun dokoki da kuma gwamnatoci .

Darakta Janar din ya bayyana haka ne yayin bude taro na 24 kan hadin gwiwa a fannin lafiyar mata masu juna biyu da jarirai da kuma yara.

Manufar taron ita ce, musayar shaidun dake nuna ci gaban da aka samu a fannin kiwon lafiyar mata da yara da matasa, ta fuskar cimma tsarin kiwon lafiya na gama gari da kuma muradun ci gaba masu dorewa.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China