Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan ta Kudu ta rasa yara 7,640 sanadiyyar cutar limonia a 2018
2019-11-13 10:24:16        cri

Cutar limonia na sanadin mutuwar yaro guda cikin kowacce sa'a 1 a Sudan ta Kudu, lamarin da ya haifar da mutuwar yara 7,640 'yan kasa da shekaru 5 a bara.

A cewar wani rahoto kan nazarin mace-macen yara da asusun kula da kananan yara na MDD da kungiyoyin Save the Children da Every Breath Counts Coalition suka hada, cutar limonia na daya daga cikin abubuwan da suka fi kashe yara a Sudan ta Kudu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar kaso 20 bisa dari na yara 'yan kasa da shekaru 5 a shekarar 2018, saboda rashin daidaito da fatara da rashin samun kiwon lafiya.

Rahoton da hukumomin suka fitar, ya ce yaran da garkuwar jikinsu ba ta da karfi saboda wasu cututtuka ko kuma tamowa da wadanda suke yankunan dake da matsanancin gurbatar iska da rashin tsabtattacen ruwa, su ne suka fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar.

A cewar daraktar kungiyar Save the Children a Sudan ta Kudu, Rama Hansraj, asibitoci a Sudan ta Kudu na fama da yawan masu cutar limonia, wadda ta yi sanadin mutuwar yara 7,000 a bara.

Kwayoyin cuta na bacteria ko virus ne ke haifar da Limonia, inda suke wahalar da yara wajen yin numfashi saboda huhunsu ya cika da kwayoyin cuta da kuma ruwa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China