Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Harkokin cinikayya na kasar Sin a ketare, ya tashi da kaso 2.4 a watanni 10 na farkon bana
2019-11-08 14:17:45        cri

Hukumar kwastam ta kasar Sin ta ce harkokin cinikayya na kasar a ketare ya samu ci gaba a cikin watanni 10 na farkon bana, ta hanyar fadada da kaso 2.4 a kan na makamancin lokacin a bara.

Hukumar ta ce a cikin wannan lokaci, yawan harkokin cinikayyar kasar Sin a ketare ya kai Yuan triliyan 25.63, kwatankwacin dala triliyan 3.67.

Kididdigar da hukumar ta fitar ta nuna cewa, yawan kayayyakin da ake fitar su daga kasar zuwa ketare ya karu zuwa kaso 4.9 yayin da wadanda ake shigo da su kasar daga ketare, ya sauka da kaso 0.4.

Kasar Sin ta samu rarar cinikayya da ya kai kaso 42.3 a kan na bara, zuwa Yuan triliyan 2.35 a cikin watannin 10. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China