Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#CIIE#Xi Jinping ya yi kira da a kafa tsarin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa da cin moriyar tare
2019-11-05 10:50:00        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da jawabi a bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyu yau Talata a birnin Shanghai, inda ya yi kira ga bangarori daban-daban da su kafa tsarin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa da cin moriyar tare.

Xi ya nuna cewa, ya kamata bangarori daban-daban su mai da hankali kan yin hakuri da juna da samun moriya tare, da kuma kokarin kiyaye dokar kasa da kasa bisa ka'idar tsarin mulkin MDD, har ma da nacewa ga tsarin kasancewar bangarori daban-daban cikin harkokin ciniki na duniya, da ingiza ciniki da zuba jari maras shinge cikin sauki, ta yadda za a gaggauta bunkasuwar tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa da yin hakuri da juna da cin moriya tare da samun daidaito. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China