Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin ya bukaci hadin kan kasashen duniya don samar da zaman lafiya a Afirka
2019-11-05 09:09:09        cri

Mataimakin wakilin din-din-din na kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya yi kira ga kasashen duniya da su hada kai wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Afirka, musamman yankin kahon Afirka.

Wu Haitao ya ce, akwai bukatar a rika warware bambance-bambance ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna. Wu ya bayyana haka ne, yayin zaman kwamitin sulhu na MDD game da zaman lafiya da tsaro a Afirka. Ya ce, kamata ya yi MDD da al'ummomin kasa da kasa su rika mutunta 'yancin kasashe, su rika shiga tsakani da shirya tattaunawar zaman lafiya, da taimakawa kasashen da ke shiyyoyi wajen amincewa da juna, da warware muhimman batutuwa ta hanyar siyasa, da samar da yanayin da ya dace na rayuwa da ci gaban mata da tashin hankali ya shafa.

Mataimakiyar babban sakataren MDD Amina Mohammed, ta yiwa kwamitin sulhun bayani game da aikin tawagar MDD da AU da ke yankin kahon Afirka, wadda ta mayar da hankali kan mata, zaman lafiya da tsaro da ci gaba.

Kan wannan batu, Wu ya bayyana cewa, har kullum kasar Sin tana goyon bayan kokarin kasashen Afirka na neman magance matsalolin dake damun nahiyar, da shigar da mata kan yadda za su taka muhimmiyar rawa wajen kare aukuwar tashin hankali da shiga tsakani. Yana mai ba da tabbacin shigar da matan cikin matakan tsara manufofi da samar da zaman lafiya da raya kasa bayan aukuwar tashin hankali.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China