Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun hallaka mayakan Boko Haram 6 yayin musayar wuta
2019-11-04 09:24:36        cri

A kalla mayakan Boko Haram 6 dakarun tsaron Najeriya suka kashe a wani musayar wuta da suka yi a daidai lokacin da 'yan ta'addan suka yi yunkurin shiga sansanin sojojin dake jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, wata majiya daga hukumar tsaron ta tabbatar da faruwar lamarin.

A daren Juma'a ne aka yi musayar wutan tsakanin mayakan Boko Haram da sojojin, yayin da suka yi yunkurin kai hari a sansanin sojoji na garin Gwon dake karamar hukumar Mafa, mai tazarar kilomita 10 daga Maiduguri, babban birnin jihar, wani babban jami'in sojojin wanda ya nemi a sakaye sunansa ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

A cewar majiyar, an shafe sa'o'i uku ana musayar wutar, inda mayakan da dama suka tsere da raunukan harsashin bindiga a jikinsu.

Wata majiyar kuma ta rawaito cewa, mayakan sun yiwa sansanin sojojin tsinke bayan sun yi amfani da manyan bindigogi 4 da babura. A yunkurinsu na shiga sansanin sojojin, sun lalata kofofin shiga sansanin sojojin biyu.

Majiyar ta kara da cewa, a martanin da suka mayar, dakarun sojojin sun tsananta binciken mayakan na Boko Haram a yankin.

Sai dai kawo yanzu rundunar sojojin Najeriya ba ta tabbatar da faruwar lamarin a hukumance ba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China