![]() |
|
2019-11-03 16:31:59 cri |
An gudanar da bikin ne a ranar Juma'a mai taken "Kawance mai girma ta al'ummomin kasa da rundunar sojojin kasar wadda ke yakar ta'addanci".
Ministan tsaron kasar Shérif Sy ya bayyana cikin jawabin da ya gabatar cewa, ba za su taba yin kasa a gwiwa ba, ko nuna gazawa ko kuma mika wuya ga duk wata barazana ba.
Ya ce mutuwar zuciya ba za ta taba samun gindin zama a zukatan sojojin kasar Burkina Faso ba.
An gabatar da bikin wanda ya samu halartar shugaban kasar Burkina Fason Roch Marc Christian Kaboré.
Kasar Burkina Faso tana fuskantar matsanancin yanayin tabarbarewar tsaro, galibi a shiyyar arewacin kasar, kusan a kullum ana samun hare haren ta'addanci wadanda ke jefa fargaba ga zukatan jama'ar kasar. (Ahmad Fagam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China