Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Uwargidan shugaban Zimbabwe ta jagoranci macin nuna adawa da takunkuman kasashen yammacin duniya
2019-10-26 16:00:37        cri
Uwargidan shugaban kasar Zimbabwe, Auxillia Mnangagwa, ta jagoranci dubban al'ummar kasar a jiya Juma'a, wajen gudanar da macin neman cire takunkuman da kasashen yammacin duniya suka sanyawa kasar shekaru 20 da suka gabata.

Kungiyar raya yankin kudancin Afrika SADC ce ta ware ranar yayin taronta na karshe da aka yi a watan Augusta, da nufin kasashe mambobin kungiyar su mara baya ga Zimbabwe, wajen kira da a cire takunkuman da aka sanya mata ba tare da gindaya sharadi ba.

Zimbabwe ta ayyana ranar a matsayin hutu, domin ba al'ummarta damar shiga a dama da su.

Wasu daga cikin masu macin na dauke da rubuce rubucen dake tir da takunkuman, in da wasu suka rubuta, "Takunkumai wani nau'i ne na bauta na zamani" da "Takunkumai laifi ne kan bil adama",wasu na cewa "Dole a cire takunkumai yanzu" yayin da wasu ke cewa "Takunkumai makamai ne na rusa tattalin arziki". (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China