Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin Sin zai samar da kudaden aikin gina tashar tekun Lekki a Najeriya
2019-10-24 09:41:56        cri

Bankin raya ci gaba na kasar Sin (CDB) zai samar da dala miliyan 629 domin gudanar da aikin gina tashar ruwan teku wanda kamfanin China Harbour Engineering (CHEC) zai gudanar da aikin, kuma shi ne aikin gina tashar ruwan teku mai zurfi irinsa na farko a Najeriya.

A lokacin bikin kaddamar da yarjejeniyar fara aikin a Legas, Biodun Dabiri, shugaban hukumar daraktoci na tashar ruwan Lekki ya ce, idan aikin ya kammala, tashar ruwan tekun Lekki za ta kasance daya daga cikin tashoshin ruwa mafiya zurfi a cikin teku ba ma kawai a Najeriya ba har ma a yankin kudu da hamadar Saharar Afrika, wacce za ta iya daukar manyan jiragen ruwan dakon kaya, kuma hakan zai baiwa Najeriya damar kasancewa babbar cibiyar harkokin fito ta ruwa a shiyyar.

A cewar Dabiri, aikin zai samar da guraben aiki na kai tsaye da wadanda ba na kai tsaye ba kimanin 170,000.

Zhang Aijun, babban jami'in bankin na CDB, ya fadawa mahalarta biki da suka hada da jami'an kamfanoni, da na gwamnati, da jami'an diflomasiyya, da sarakunan gargajiya cewa, Afrika tana taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa harkokin kasuwancin bankin na CDB a duniya baki daya.

A cewarsa, bankin CDB yana fatan wannan aikin zai kasance a matsayin wani tushen fadada harkokin kasuwancinsa a Najeriya kuma yana burin ba da gudunmowa wajen bunkasa ci gaban tattalin arzikin Najeriya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China