Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dandalin Xiangshan ya samar da shirin Sin na kiyaye zaman lafiyar duniya
2019-10-23 20:05:29        cri

A cikin wasikar murnar bude taron dandalin tattaunawar Xiangshan karo na 9 da aka shirya a nan birnin Beijing da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike, ya jaddada cewa, kasarsa ta himmatu wajen inganta hadin kai ta hanyar yin shawarwari, da inganta zaman lafiya ta hanyar hadin kai, da kuma tabbatar da samun ci gaba cikin lumana, kana ya jaddada matsayin kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan kiyaye tsarin kasa da kasa karkashin jagorancin MDD, da kara kyautata sabuwar dangantakar tsaro. Baya ga haka, ya gabatar da bukatar kafa tsarin tsaro dake dacewa da hakikanin yanayin da kasashe daban daban ke ciki, da yanayin musamman da sassan duniya ke ciki, hakan nan kuma ya samar da ra'ayinsa game da karfafa hadin kan kasa da kasa a fannin tsaro, da ma shirin kasar Sin na kiyaye zaman lafiya a yankin Asiya da tekun Pasific da duniya baki daya.

Manufofin da shugaba Xi ya gabatar sun dace da bukatun kasashe daban daban na tabbatar da zaman lafiya, ci gaba da kuma hadin kai, abin da mahalarta taron suka mai da martani sosai a kansu.

Nan gaba kuma, kasar Sin za ta ci gaba da martaba sabon tsarin tsaro mai dorewa mai salon hadin kai, da tsayawa kan manufar tsaron kasa dake dacewa da tsaron kai, kana da tsarin tabbatar da zaman lafiyar duniya, da ba da gudummowa ga ci gaban duniya, da kiyaye tsarin kasa da kasa, za kuma ta kara karfinta na inganta raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil- Adam. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China