2019-10-23 13:26:20 cri |
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, da takwaransa na kasar Switzerland Ignazio Cassis, sun gana da manema labaru a jiya Talata, inda Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin babbar kasa ce da ke sauke nauyinta yadda ya kamata. Kuma ba ta boye komai ga kasashen duniya, kana tana kiyaye zaman lafiya da kuma kara azama kan ci gaba.
A yayin taron, an tambayi ra'ayin kasar Sin dangane da soke-soken da wasu 'yan siyasan kasar Amurka suka yi wa kasar ba bisa wani dalili ba. Inda Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ba ta taba dogaro da karfin soja ba, kuma ba ta taba tayar da yake-yake kan kasashen waje ba, haka kuma ba ta taba mamaye yankin wata kasa ba.
Ya ce har kullum, kasar Sin na tsayawa kan daidaita takaddamar yankuna da moriyar da ke tsakaninta da wasu kasashe ta hanyoyin tattaunawa da shawarwari cikin lumana.
Wang ya kara da cewa, kasar Sin tana kokarin hadin gwiwa domin amfanar kowa. Ba kanta kadai take rayawa ba, har ma da ba da gudummowa wajen bunkasa tattalin arzikin duniya da kaso 30 ko fiye da haka a ko wace shekara. kuma ta zama muhimmin jigon farfado da tattalin arzikin duniya. Ya ce kasar Sin tana tsayawa kan sauke nauyin da kasashen duniya suka dora mata, da cika alkawarinta a tsanake. Sannan, kasar Sin tana tabbatar da adalci kan dukkan kasashen duniya, tare da girmama kowa. Haka zalika, kasar Sin ba ta dora wa sauran kasashe laifi, kuma ba ta sanya dokokinta gaba da dokokin kasa da kasa, ba kuma ta sanya takunkumi na gashin kai kan sauran kasashe ko kuma bisa dokokin da take aiwatarwa a cikin gida. (Tasallah Yuan)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China