2019-10-23 10:53:27 cri |
Sakatare Janar na ma'aikatar, Wilfred Gbasa Nyongbet, ya shaidawa manema labarai cewa, gwamnati na son yi wa tsarin ilimin manyan makarantu garambawul tun daga tushe, ta yadda zai dace da samar da aikin yi.
Ya ce aiwatar da sauyin na nufin, wanda ya koyi tarihi ko adabi ko kimiyyar siyasa, na da damar zama kwararre.
Wilfred Nyongbet, ya ce gwamnati na da Muradin inganta sabuwar fasahar sadarwa, yana mai jaddada cewa, za a bude cibiyoyin fasahohin zamani a jami'o'i 8 na jihohin kasar.
Ya kara da cewa, gwamnatin na fatan sabon tsarin zai zamar da ingantaccen ilimi ga daliban jami'o'i, wadanda za su zamo masu samar da aikin yi. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China