2019-10-22 09:54:58 cri |
Tsarin ilmin manyan makarantun ilmin kasar Sin ya kara samun cigaba matuka a cikin shekaru 20 din da suka gabata, inda a cikin wannan wa'adin an samu yawan jami'o'i da manyan kwalejojin ilmi a fadin kasar Sin kimanin 2,663 ya zuwa shekarar 2018, inda ya ninka sama da sau 1.6 daga shekarar 1998, a cewar rahoton wanda aka gabatar a taron da ake gudanarwa a duk bayan watanni biyu-biyu na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin (NPC).
Adadin dalibai Sinawa dake shiga manyan makarantun ilmin kasar Sin ya karu daga miliyan 8.5 a shekarar 1998, zuwa miliyan 38.33 a shekarar 2018, inda adadin ya karu da kashi 48% na daliban manyan makarantun 'yan tsakanin shekaru 18 zuwa 22 na haihuwa ya zuwa shekarar 2018, a cewar rahoton. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China