Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alkaluman GDP na kasar Sin ya karu da kaso 6.2 a rubui 3 na farkon bana
2019-10-18 14:08:37        cri

Yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasar Sin ya karu da kaso 6.2 a rubu'i 3 na farkon bana, zuwa yuan triliyan 69.78, kwatankwacin dala triliyan 9.87.

Ci gaban da aka samu ya yi daidai da hasashen da gwamnatin kasar ta yi na kaso 6 zuwa kaso 6.5 a bana. Inda a rubu'i na 3, karuwar GDPn kasar ta tashi zuwa kaso 6.

Yayin wani taron manema labarai, hukumar ta ce tattalin arzikin kasar na ci gaba da tafiya ba tare da wata tangarda ba, duk da ta tabbatar da cewa kasar na fuskantar matsin lamba, biyo bayan karuwar rashin tabbas da tafiyar hawainiya da tattalin arzikin duniya ke yi. (Fa'iza)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China